Babu tilascin da muka dora wa kowa kan bayar da shaida a shari’ar badakalar aikin lantarkin Mambila - Fadar Shugaban Nijeriya


Fadar shugaban kasa ta musanta rahotannin dake cewa an tilasta wa tsohon shugaban kasa Muhammad Buhari ko wani dan NIjeriya domin ya bayar da shaida a gaban kotun sasanta rikici dake zamanta a birnin Paris na Faransa.

Da yammacin jiya Asabar ne wata jarida ta ruwaito cewa an kai wa Buhari sammaci domin ya bayar da shaida akan rikicin da ake yi na kwangilar aikin wuta na mambila ta dala biliyan 6.

Sai dai a martani na gaggawa, mai magana da yawun Shugaba Tinubu Bayo Onanuga, ya ce wannan ba gaskiya bane, amma bai musanta cewa kotun na sauraren karar ba.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp