Sanata Rabiu Musa Kwankwaso |
Shugaban jam’iyyar NNPP Hashim Sulaiman Dungurawa, ya yi kira ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya sake duba ga manufofin gwamnatinsa da al'umma ba sa goyon baya, ko kuma ya fuskanci shan kaye a babban zabe mai zuwa.
Dungurawa ya kuma ce batun da ake cewa jagoran jam'iyyar Rabiu Musa Kwankwaso na shirin sauya sheka zuwa jam’iyyar APC ba gaskiya ba ne.
Da yake zantawa da manema labarai a ranar Alhamis, Dungurawa ya jaddada cewa jam’iyyar NNPP na kara samun tagomashi tare da kara fadada a dukkan jihohin Nijeriya 36, wanda hakan zai basu damar samun kujerun gwamnonin wasu jihohi a zaben 2027.
Ya bukaci gwamnatin tarayya da ta mayar da hankali wajen aiwatar da manufofin da za su rage wa ‘yan Nijeriya radadin da suke ciki da kuma kauce wa bullo da tsare-tsaren da suka saba wa muradun jama’a.