Wasu 'yan Nijeriya mazauna kasashen waje sun soki rahoton kungiyar dake bincike kan cin hanci da rashawa a duniya OCCRP, da ya sanya shugaban Nijeriya Bola Tinubu cikin shugabanni masu aikata rashawa a 2024.
Tsohon shugaban kungiyar magoya bayan jam'iyyar APC a kasashen waje, Ayoola Lawal, ne ya nuna tantama kan rahoton.
A cewarsa mafi yawan zarge-zargen da ake yi wa Tinubu babu wata hujja da za ta tabbatar da su, kamar yadda DW Africa ta ruwaito.
Category
Labarai