Babu hannunmu a sulhu da 'yan ta'adda - Gwamnatin jihar Katsina

 

Malam Dikko Umaru Radda

Gwamnatin jihar Katsina ta musanta cewa tana wata tattaunawa domin yin sulhu da ‘yan bindiga.

Kwamishinan yada labarai da al’adu na jihar,Dr Bala Salisu ya bayyana hakan a wata tattaunawa da ya yi da Daily Trust ta wayar tarho inda yace gwamnatin nayin duk mai yuwuwa wajen yakar 'yan bindiga.

Dr. Bala ya nanata aniyar gwamnatin jihar na karbar duk wani dan bindiga da daya mika wuya tare da yin watsi da fashi da satar mutane.Ya kara da cewa babu wata yarjejeniya da suka kulla kuma babu wani da suka zauna dashi domin yin sulhu,a cewar sa gwamnati ba za ta nemi wani dan ta'adda domin yin sulhu da shi ba.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp