Kamar yadda jaridar Punch ta rawaito faduwar da layin wutar lantarkin ya yi ta haifar da rashin wuta a fadin kasar baki daya.
Faduwar layin wutar lantarkin dai shi ne karo na 13 a cikin watanni 13 da suka gabata.
Binciken da jaridar Punch ta yi,ya nuna cewa wutar lantarki ta ragu daga megawatts 2111. zuwa megawatts 390.20 da karfe 3 na yamma cin ranar Asabar.