Babban hafsan sojin Nijeriya Christopher Musa yayi alkawarin ingata tsaro a shekarar 2025

 

Janar Christopher Musa

Babban hafsan sojin Nijeriya Janar Christopher Musa, ya yi alkawarin inganta tsaro a fadin Nijeriya a shekarar 2025.

Janar Musa ya yi wannan alkawarin ne yayin wata ziyara da ya kai wa dakarun, Operation safe haven, a garin Samaru dake karamar hukumar Zangon Kataf, ta jihar Kaduna, a ranar Alhamis.

A yayin ziyar ya bayyana cewa shekarar 2024 ta kasance shekara mai cike da kalubale ga sojoji amma ya ba da tabbacin cewa shekarar 2025 za ta zo da sakamako mai kyau tare da samun sauyi a fannin tsaron Rayuka, Dukiyoyin al'umma.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp