Babban Hafsan Sojin kasa COAS, Olufemi Oluyede, ya amince da canjawa manyan hafsoshi a Nijeriya wajen aiyyu

 



Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami'in hulda da jama’a na rundunar, Onyema Nwachukwu, ya fitar ranar Asabar a Abuja.


Nwachukwu, ya bayyana cewa, sake tura sojoji wani shiri ne na inganta aiki ayyukan rundunar.

Ya ce jami’an da abin ya shafa sun hada da kwamandojin rundunar, manyan hafsoshi, manyan kwamandojin (GOC), kwamandojin cibiyoyin horar da sojoji, birgediya da sauran manyan mukamai.

 A cewarsa, sake tura dakarun da kuma sauyawa wasu wuraren aiki na nuni da kudurin rundunar na tabbatar da tsarin jagoranci da zai iya magance matsalolin tsaro a fadin kasar.

Mista Nwachukwu ya ce wasu daga cikin manyan hafsoshin da aka canza wa wajen a hedkwatar sojojin sun hada da Manjo Janar Lawrence Fejokwu, daga Kwalejin Tsaro ta kasa zuwa sashin kula da harkokin soji, wanda aka nada shi Shugaban Gudanarwa na rundunar Soji.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp