Ba wani siddabarun da zai sa Tinubu faduwa zabe a 2027 - Saleh Zazzaga

Shugaban kungiyar gamayyar kungiyoyin magoya bayan jam'iyyar APC na Arewa ta tsakiyar Nijeriya Hon Saleh Abdullahi Zazzaga ya bayyana cewa babu wani siddabarun da zai iya sa Shugaba Tinubu ya fadi zabe a shekarar 2027.

A cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja, Saleh Zazzaga ya ce 'yan Nijeriya za su yi wa Shugaba Tinubu ruwan kuri'u a shekarar 2027, ganin yadda tsare-tsaren gwamnatinsa za su kara daga darajar Nijeriya musamman idan zaben ya gabato.

Shugaban kungiyar wanda yana cikin kwamitin yakin neman zaben Shugaba Tinubu a zaben da ya gabata, na martani ne kan kalaman shugaban jam'iyyar NNPP na jihar Kano Hashimu Dungurawa da ya gargadi Shugaba Tinubu cewa ya shirya faduwa zabe idan ya kullaci cewa zai sake tsayawa takara a 2027.

Sai dai sanarwar Hon Saleh Zazzaga ya nace cewa babu abin da zai sa jam'iyyar APC faduwa zabe, don haka, Shugaba Tinubu zai sake kasancewa shugaban Nijeriya a wa'adi na biyu bayan zaben 2027.

Zazzaga ya ce, manyan matakan da Shugaba Tinubu ya dauka na cire tallafin mai da kokarin inganta darajar Naira, duk za su sa kasar kan turba ta gari ne ba wai shafa-labari-shuni ba.

Ya ma ce ya kamata a yaba wa Shugaba Tinubu da ya dauki wadannan matakan, wanda a cewarsa gwamnatocin da suka gabata suka gaza aiwatarwa. Ya ci gaba da cewa 'yan Nijeriya za su riba ci wadannan matakai ba da jimawa ba.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp