Babbar jam’iyyar adawa ta Nijeriya PDP a yankin Arewa masu gabas ta gudanar ta taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar da ya gudana a jihar Bauchi.
Taron dai ya samu halartar dukkanin gwamnonin ta uku da suka hada da gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed da na jihar Taraba Dr Agbu Kefas da kuma Ahmad Umar Fintiri na jihar Adamawa.
Haka kuma taron ya samu halartar Sanatoci da ‘yan majalissun wakilai da kuma ‘yan majalisar jiha daga shiyyar.
Sai dai rahotanni sun bayyana cewa tsohun shugaban kasar Atiku Abubakar bai samu halartar taron ba ko aike wa da wakili a wajen taron.
Wannan dai a iya cewa ko bai rasa nasaba da rikicin cikin gida da jam'iyyar ta PDP ke fama da shi.