Ba da gan-gan harin da muke kai wa 'yan ta'adda ke shafuwar fararen hula ba - Sojojin Nijeriya
Rundunar sojin Najeriya ta ce duk hare-hare ta sama da take kai wa ga masu aikata laifukan ne ba fararen hula ba.
Babban Hafsan Sojojin Najeriya Janar Christopher Musa ne ya bayyana haka a wata hira da yayi a gidan Talabiji na Arise TV, a lokacin da yake mayar da martani game da mutuwar fararen hula sama da 10 sanadiyar harin da sojojin suka kai kwanan nan a Zamfara.
Janar Christopher Musa, wanda ya bayyana cewa sojoji sun bi ka’idoji masu tsauri kafin aiwatar da duk wani hari ta sama, ya jaddada cewa sojojin na kai hare-hare ta sama daidai gwargwado domin kawar da yan ta'adda dake addabar wasu sassan jihohin Nijeriya.
Allah kayimuna magani
ReplyDelete