![]() |
Gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni |
Yan bindigar ana zargin sun kai farmaki kasuwar da ke ci duk sati a Ngalda karamar hukumar Fika da misalin karfe 6 na yammacin ranar Litinin da suka yi harbe harbe tare da fasa shaguna a kasuwar.
Wani dan karamar hukumar Fika Dauda Yakubu Damazai, ya shaida wa Daily Trust cewa wasu ‘yan kasuwa guda bakwai a babbar kasuwar shanun sun rasa rayukansu a wannan mummunan hari.
Ya ce da yammacin ranar wasu da ba a san ko su waye ba sun kai hari a kasuwar shanu da babbar kasuwar inda suka kashe mutane bakwai tare da jikkata mutane 11, kuma tuni aka garzaya da su babban asibitin Fika domin duba lafiyar su.