'Yan sanda |
An kama wata mata mai suna Fatima Dzuma 'yar kimanin shekaru 27 bisa zargin ta da ajalin mijinta Baba Aliyu mai shekaru 25 a jihar Neja.
Lamarin dai ya faru ne a kauyen Lafiyagi Dzwafu da ke karamar hukumar Katcha ta jihar, a lokacin da ake shirye shiryen bikin nadin sunan dansa da matarsa ta farko ta haifa masa.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Neja, Abiodun Wasiu, ya ce an kama Fatima ne bayan an gano gawar mijinta a wani daji da ke kusa da gidansu, kwanaki uku bayan an nemeshi an rasa.
A wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma'a, kakakin 'yan sandan ya ce wadda ake zargin ta amsa laifin da ake tuhumar ta da shi, inda ta ce a lokacin da mijin ta yake barci ta halaka shi, sannan ta daure shi da igiya kafin ta jefar da gawar a cikin daji.