Amarya da Ango |
Lamarin ya faru ne a karamar hukumar Jahun da ke jihar Jigawa.
Wasu shaidun gani da ido sun shaida wa jaridar PUNCH cewa,ana zargin wani dan kasuwa ne ya sa amaryar ta aikata hakan.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Shi’isu Adam, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma ce ana ci gaba gudanar da bincike akai.
A cewar sa 'yan sanda sun kama wasu mutane biyu da ake zargi da laifin sanya guba a cikin abincin, wadanda ake zargin su biyun amaryar ce da wata mace, ya kara da cewa suna tsare kuma ana yi musu tambayoyi daga sashin binciken manyan laifuka na rundunar.