![]() |
Victor Osimhen |
A cewar kafar yada labaran Turkiyya, Posta, lamarin ya faru ne a lokacin da Osimhen, ke barin wani gidan shakatawa na dare tare da abokansa.
Dan jaridan, Tolga Bozduman, ya tabbatar da cewa, lokacin Osimhen yake fitowa daga gidan shakatawar , ya na cikin daukar sa Bidiyo , dan wasan ya yi masa kakkausan lafazi kan daukar ta sa da ya yi.