Ganduje/Peter Obi |
Dan takarar shugaban kasa na Jam'iyyar Labour Party a zaben 2023 da ya wuce Peter Obi ya ce kalaman da mai magana da yawun jam'iyyar APC Felix Morka ya yi a baya bayan nan ya saka shi shida iyalin sa cikin hadari.
Sai dai a bagare daya shugaban shugaban jam'iyyar APC Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana kalaman na Obi, a matsayin neman bata suna.
A cikin wata sanarwa da Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya sanya wa hannu, ya bayyana batun a matsayin abin takaici da bisa ikirarin da Peter Obi ya yi cewa ana yimasa barazana shi da iyalinsa.