Mambobin majalisar dokokin jihar Lagos sun tsige shugaban majalisar Mudashiru Obasa.
Hakama an nada mataimakiyarsa Mojisola Meranda, a matsayin wadda za ta maye gurbinsa, mace ta farko da ta riki mukamin a jihar Lagos.
Tsige Mudashiru Obasa na zuwa ne kasa da wata daya da aka zarginsa da kashe naira biliyan 17 wajen gyara kofar shiga majalisar.
Category
Labarai