An sako wasu mata 'yan Nijeriya bayan shafe watanni 10 tsare a Saudiyya bisa zargin safarar kwayoyi


Ma'aikatar harkokin wajen Nijeriya ta sanar da sakin wasu mata uku 'yan Nijeriya da aka gurfanar a kasar Saudiyya bisa zargin safarar miyagun kwayoyi, bayan sun shafe watanni 10 a tsare gidan kaso.

Sanarwar da mai magana da yawun ma'aikatar Kimiebi Ebienfa ya fitar, ta tabbatar da sako matan bayan an bi hanyoyin diflomasiyya.

A watan Maris na 2024 ne aka damke Hadiza Abba, da Fatima Umate Malah, da kuma Fatima Kannai Gamboil a filin jirgin saman kasa da kasa na Yarima Mohammad bin Abdulaziz da ke birnin Madinah.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp