An rage shigo da tataccen mai daga Turai bayan bude matatar man Dangote a Nijeriya - OPEC


Kungiyar kasashen dake fitar da arzikin mai ta OPEC , ta ce fara tace man fetur da dangogin sa da matatar mai ta Dangote ta fara ya rage yawan shigo da tataccen mai daga Turai.

Ta cikin rahoton wata -wata na kasuwar mai da dangogin sa da aka wallafa a ranar 15 ga Janairun 2025, kungiyar ta OPEC , ta ce samar da wadataccen man daga matatar ta Dangote ya sa tilas yanzu wasu kamfanonin su nemi kasuwa a wasu guraren.

Haka zalika rahoton ya ce shigowar matatar a kasuwar duniya da sauye -sauyen da ta samar zai kawo gagarumin kalubale ga kasuwar mai ta duniya

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp