Hukumar dake kula da babban birnin tarayya Abuja ta haramtawa sana'ar jari bola a fadin jihar
Kwamishinan ‘yan sanda a babban birnin tarayya, Olatunji Disu ne ya sanar da haramcin yayin da yake zantawa da manema labarai, bayan gudanar da taron kwamitin tsaro na babban birnin tarayya Abuja
Olatunji Disu ya ce, daga yanzu wuraren zuba shara dake bayan gari kawai aka amince masu sana'ar su rika harkokinsu.
Ya kuma ce dukkan hukumomin tsaro za su tabbatar da cewa an aiwatar da wannan umarni daga ranar 14 ga watan Janairun da muke ciki.