Shugaban Amurka Joe Biden, ya ba da sanarwar tallafin dala $770 ga al'ummar yankin Los Angeles da wutar daji mafi muni a tarihin jihar Califonia ta shafa.
Joe Biden, wanda ke dab da barin fadar White House, ya bayyana hakan ne a ranar Litinin.
Bayanai sun nuna cewa gobarar dajin ta yi sanadin mutuwar mutane 29, kuma Amurkawa na ci gaba da nuna fargaba.