Al'ummar jihar Kano za su yi wa Shugaba Tinubu ruwan kuri'u a zaben shekarar 2027 - Wani jigon jam'iyyar APC

 

Shugaba Tinubu/Dr,Abdullahi Umar Ganduje


Jigo a jam'iyyar APCn jihar Kano Engr.  Rabiu Bichi ya bayyana cewa al’ummar jihar Kano za su zabi jam’iyyar APC a zaben 2027, inda ya ce shugaba Bola Tinubu ne zai lashe jihar da gagarumin rinjaye.

Bichi ya yi wannan jawabi ne a Kano lokacin da wata kungiyar jam'iyyar APC a Kanon ta shirya wani taro domin karrama wasu mutane uku da shugaba Tinubu ya nada tare da yaba wa shugaban kasa kan yadda ya dauki 'yan jihar a gwamnatinsa.

A jawabin na sa Bichi ya ce dama can jam'iyyar NNPP da ke mulki a jihar bata da farin jini saboda wasu manufofi da ta ke da shi.

Ya bayyana cewa suna hada magoya bayansu da suka hada da matasan jam’iyyar APC gabanin 2027 domin shugaba Tinubu lashe zaben.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp