![]() |
Shugaban Nijeriya sanye da rigar Super Eagles |
Tawagar kwallon kafa ta Najeriya Super Eagles ta samu kanta a rukunin C bayan raba jadawali na rukuni a gasar Kofin nahiyar Afrika, AFCON ta 2025 da za a yi a kasar Morocco.
Daga cikin abokanan karawar ta Super Eagles a rukunin akwai kasar Tunisia sai Uganda da Tanzania.
Kasashen da ke rukunin A sun kunshi Morocco mai masaukin baki sai Mali da Zambia kana Tsibirin Comoros.
Daga rukunin B kasashen Masar wato Egypt da Afirka ta Kudu sai Angola da Zimbabwe ne za su kece raini.
Rukunin D akwai kasar Senegal da Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango sai Jamhuriyar Benin da Botswana.
Rukunin E na dauke da kasashen Algeria da Burkina Faso sai Equatorial Guinea da Sudan. Sai rukunin karshe na F mai kasashen Cote d'Ivoire kana Cameroun da Gabon tare da Mozambique.