Kwamishinan kananan hukumomi da sha'anin masarautu na jihar Kano Alhaji Tajo Usman , ya ce adalci da shugabanci na gari na gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf ya sa ya dawo da kudi da suka yi rara har miliyan 100.
Kwamishinan ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai ranar Jumma'a a Kano.
Alhaji Tajo Usman, ya ce bai yi zaton gwamnan zai bayyanawa Duniyae abinda ya yi ba kasancewar yayi ne domin koyi da halaye nagari irin na gwamnan.
Kwamishinan wanda tsohon jami'in hukumar hana fasakwauri ta Najeriya wato Custom ne , ya samu sam barka tare da jawo cece kuce bayan da ya mayar da rarar naira miliyan 100, na kudaden samar da tufafin daliban firamare.