Kungiyar kasashen yammacin Afirka ta ECOWAS, ta umurci mambobinta da su ci gaba da mu'amala da kasashen Burkina Faso, Mali da Jamhuriyar Nijar.
Wannan na zuwa ne bayan da kungiyar ta amince da fitar kasashen uku da ga cikin ECOWAS a hukumance da yau Laraba 29 ga watan Janairun 2025.
Wata sanarwar da kungiyar ta fitar a Laraba, ta ce ficewar kasashen ba zai hana ci gaba da mu'amala tsakanin al'ummar kasashen ba ciki har da harkokin kasuwanci da shige da fice.
Tuni dai kasashen na Burkina Faso, Nijar da Mali suka kafa sabuwar kungiyar kawance da suka kira Alliance des États du Sahel (AES) (AES) a madadin ECOWAS.
Category
Labarai