Sarkin Kano na 16 Muhammad Sanusi II, ya bayyana takaicinsa akan yadda aka sauya masa kalamai cewa ba zai taimaki gwamnatin shugaba Tinubu ba domin aiwatar da tsare-tsarenta.
A cikin wani sako da ya wallafa a shafin X, Muhammadu Sanuni II ya ce dogon jawabin da ya yi ne aka gutsure zuwa rubutun da bai wuce sakin layi ba.
Sarkin Kano na 16 ya ce jawabinsa na goyon bayan tsare-tsaren gwamnatin Tinubu ne kuma ya jinjina wa 'yan Nijeriya akan hakurin da suka yi na wadaka da dukiyarsu a baya.
Category
Labarai