Gwamnatin Tarayyar Nijeriya da kakkausar murya, ta sa kafa ta shure zarge-zargen Shugaban mulkin soja na Nijar Janar Abdourahmane Tiani ya yi ma cewa akwai wata boyayyiyar alaka tsakanin Nijeriya da kasar Faransa.
An dai ga faifan bidiyon Tiani na yawo a kafafen sada zumunta, inda ya ke zargin cewa akwai wata alaka da ake yi wa nuku-nuku tsakanin Nijeriya da Faransa.
A cikin wata sanarwa daga Ministan yada Labaran Nijeriya Mohamed Idris, da DCL Hausa ta samu kwafi, ta ce zancen-zuci ne kawai Janar Tiani ke sakawa, amma babu wata boyayyiyar alaka tsakanin kasashen biyu da ma kowace kasa da ke da barazana ga kasar Nijar.
Sanarwar ta ce a matsayin Shugaba na Tinubu na shugaban kungiyar ECOWAS ya nuna dattako da iya tafiyar da lamurra, har ma aka bar kofar sasanci na Nijar da sauran kasashe na su koma cikin kungiyar.