Zaben Amurka, sabon taken Nijeriya da rumbun lantarki na kasa, na cikin abubuwan da 'yan Nijeriya su ka fi nema a shafin Google a 2024


Kamfanin Google ya fitar da jadawalin abubuwan da 'yan Nijeriya suka fi nema a kan shafin a shekarar 2024 da muke bankwana da ita.

Bayanin da kamfanin ya fitar a ranar Talata, ya nuna cewa 'yan Nijeriya sun fi mayarda hankali akan abubuwan da suka shafi siyasa da tattalin arziki.

Tambayar da ta fi shigewa 'yan Nijeriya duhu ita ce 'Nawa ne farashin dala zuwa naira a yau?'

Ga jerin abubuwan da aka fi nema a Google cikin shekara ta 2024:

1. Zaben Amurka (US elections)
2. Sabon taken Nijeriya (New national anthem)
3. Rumbun lantarki na kasa (National grid)
4. Albashi mafi karanci (Minimum wage)
5. Fashewar wani abu a Ibadan (Ibadan explosion)
6. Zaben jihar Edo (Edo state election)
7. Zanga-zanga a Nijeriya (Protest in Nigeria)
8. Yajin aikin 'yan kwadago (Labour strike)

Da dai sauransu.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp