Za a kara adadin lantarkin da ake samarwa nan da watan Janairu - Ministan lantarki


Ministan lantarki, Adebayo Adelabu, ya ce ana ci gaba da shirye-shiryen samar da karin megawatts 150 na wutar lantarki a Nijeriya nan da watan Janairun 2025.

Ministan ya bayyana haka ne a fadar shugaban kasa ranar Laraba, inda ya ce matakin zai magance matsalolin da ake fuskanta na katsewar manyan tashoshin lantarki a fadin kasar.

Adelabu, wanda ke cikin ganawar da aka yi tsakanin shugaba Bola Ahmed Tinubu da takwaransa na Jamus, Frank Walter Steinmeier, ya ce hanyar da za a bi wajen tabbatar da samar da wutar lantarki shi ne hadin gwiwa, da kuma sabunta manyan tashoshin samar da lantarki. 

Ya ce tuntuni Nijeriya da Jamus suna da dadaddiyar alaka a fannin makamashi da wutar lantarki, saboda akwai bukatar sabunta wannan alaka.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp