'Yan sanda sun rufe kofar shiga Masarautar Bichi


Jami'an tsaron 'yan sanda sun rufe kofar shiga masarautar Bichi gabanin zuwa Sabon Hakimin yankin.

Jami'an kuma sun umurci masu unguwannin da suka taro domin tarbonsa su fice daga masarautar.

Sai dai shugaban karamar hukumar Bichi Alhaji Hamza Mai fata, ya sanarda dage ranar tarbon sabon hakimin da aka shirya yi a yau Jumu'a tare da kira ga al'umma su kasance masu bin doka da oda.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp