Rundunar 'yan sandan babban birnin tarayya Abuja ta sanar da kama wasu mutane biyu da zargin suna kiransu kansu da sojoji, amma na bogi ne.
Rundunar 'yan sandan a taron manema labarai da CP Olatunji Rilwan Disu ya kira, ya ce an kama mutanen Emmanuel Linus da Moses Daniel a ranar 30 ga watan jiya na Nuwamba, 2024.
CP Disu ya ce an kama mutanen ne sanye da kayan sojoji. Yayin da 'yan sanda ke bincikensu, Linus ya gabatar musu da katin shaida na bogi mai dauke da shekarar haihuwa 20 ga watan Disamba, 2024.
Kan haka rundunar 'yan sandan ta bukaci daukacin jama'a da su kasance cikin ankarewa a yayin gudanar da ayyukansu don gudun fadawa hannun bata-gari.