Jami'an 'yan sandan kasar Koriya ta Kudu sun kai samame a ofishin shugaban kasar, a ci gaba da bincike kan dokar soja da shugaban ya ayyana.
Hakama masu kula da gidan gyara hali na kasar sun ce, ministan tsaron kasar ya yi kokarin kashe kansa jim kadan bayan kama shi.
A wannan Larabar, jami'an tsaro na musamman sun kai samame a ofishin shugaban kasar Koriya ta Kudu da na rundunar 'yan sanda ta kasa da ta yankin Seoul, da kuma jami'an tsaron majalisar dokokin kasar.