Rundunar 'yan sandan jihar kano ta ce cikin shekarar 2024 da muke bankwana da ita ta kama wayoyi guda 415 a hannun masu kwacen waya a fadin jihar.
Kakakin rundunar SP Abdullahi Haruna kiyawa ne ya bayyana hakan ga manema labarai a hedkwatar hukumar a ranar Talata.
Kiyawa ya ce hukumar 'yan sandan a shirye take ta ci gaba da fatattakar 'yan daba tare da masu kwacen waya a jihar muddin basu daina ba.
Category
Labarai