Wasu masu gidan sayar da giya a Bwari da ke Abuja, sun ce sun ci riba mai kyau a bukuwan Kirsimeti duk kuwa kukan da wasu 'yan Nijeriya ke yi na matsin rayuwa.
Suka ce hakan ta faru ta yadda mutane suka sha giyar mai tarin yawa a lokacin bukukuwan kamar yadda kamfanin dillancin labaran Nijeriya NAN ya rawaito