Hukumar Kididdiga ta Nijeriya NBS ta ce yanzu haka kimanin mutane miliyan 1 da dubu 134 da 828 daga gidaje dubu 251da 82 ne ke gudun hijira a kasar.
NBS ta bayyana hakan ne a wani rahoto da ta fitar a baya-bayan nan, inda ta bayyana jihar Borno a matsayin wadda ta fi kowacce yawan mutanen da ke gudun hijira da yawansu ya kai dubu 877 da 299, kwatankwacin kashi 77 da digo 3 na daukacin al’ummar jihar da aka kidaya.
Rahoton ya kuma bayyana cewa an gudanar da binciken ne a shekarar 2023 a jihohin Adamawa da Yobe da Borno da Sokoto da Katsina da Benue da Nasarawa.
Category
Labarai