Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya ce 'yan kasar na rayuwar karya da hakan ya sa tattalin arzikin kasar ya yi mummunar faduwa kafin ya hau mulki ya cire tallafin man fetur.
Shugaban kasar ya ce akwai bukatar a ceto kasar daga yunkurin durkushewa da ya sanya ala-tilas sai an bullo da hanyoyi da dabarun da za su iya rike ta irinsu cire tallafin man fetur da kokarin daidaita canjin kudi.
Shugaban kasar da ya samu wakilcin shugaban jami'ar Ilorin Prof Wahab Egbewole, ya yi wannan furucin ne a wajen taron yaye dalibai karo na 34&35 na jami'ar tarayya da ke Akure jihar Ondo a karshen mako in ji jaridar Daily Trust.