Hukumar kula da shirin inshorar lafiya ta Nijeriya ta ce 'yan kasar 19.2 ne su ka yi rajista a karkashin shirin, adadin da ya zarce wanda ta yi hasashen samu a cikin shekara ta2014.
Darakta Janar na hukumar NHIA, Dr Kelechi Ohiri ne ya bayyana hakan a Abuja, lokacin wani taron ranar kula da lafiyar al'umma ta duniya domin bita akan irin ci gaban da ake samu a bangaren kiwon lafiya.
A cewarsa, da wannan nasarar da Nijeriya ta samu na waɗanda suka shiga tsarin inshorar lafiya, ta cimma kashi 95 na hasashen da take son samu a shekarar 2027.
Category
Labarai