A ranar 31 ga watan Disamba 2023, ajalisar wakilan Najeriya za ta gabatar da tallafin naira milyan N704.91 ga Shugaba Bola Tinubu domin amfani da kudin wajen ragewa talakawa radadin cire tallafin man fetur.
Idan za a iya tunawa, ranar 18 ga watan Yuli majalisar ta amince a ware kashi 50 da ga dubu 600 na albashin kowane dan majalisa har tsawon watanni 6 domin magance matsalolin da talakawa ke fuskanta.
A zaman majalisar na yau, Tajuddeen Abbas, Kakakin majalisar ya ce zai jagoranci tawagar da za ta mikawa shugaban kasa kuɗaɗen kamar yadda a ka yi alkawari.