Kungiyoyin kwadago a jihohin Kaduna da Zamfara, sun janye yajin aikin da su ka shiga saboda takaddama akan aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi.
A jihar Kaduna, NLC ta janye yajin aikin tare da baiwa gwamnati wa'adin kwana bakwai domin gyara tsarin biyan sabon mafi ƙarancin albashin naira 72,000 da kungiyar ta ce akwai kura-kurai a ciki.
Yayinda a Zamfara kuwa, kungiyar kwadago NLC ta janye yajin aikin da ta fara kwana biyu da suka gabata, bayan da gwamnatin jihar ta amince da biyan naira 70,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi.