Kabiru Onyene makusancin tsohon gwamnan Kogi |
Rahotanni daga jihar Kogi na nuni da cewa, an sace Kabir Onyene, ne da misalin karfe 7 da mintuna 5 na yammacin ranar Litinin, lokacin da wasu ‘yan bindiga dauke da bindigogi suka farmaki ofishinsa da ke Okene a jihar, inda suka yi ta harbe-harbe kafin daga bisani su yi awon-gaba da shi.
Bayanai sun nuna cewa yayin harin, an harbe wani mutum wanda kawo yanzu ba a tantance ko wanene ba.
Sai dai har kawo yanzu rundunar ‘yan sandan jihar ta Kogi ba ta ce uffan, kan lamarin ba.
Category
Labarai