Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kai hari kan mahaifiyar gwamnan jihar Taraba, Jumai Kefas da kuma ‘yar uwar sa, Atsi.
Lamarin ya faru ne a jiya a kan hanyar Wukari zuwa Kente a karamar hukumar Wukari
Shugaban karamar hukumar Wukari Dauda Samaila Agbu ya tabbatar da faruwar lamari inda ya bayyana shi a matsayin "mai matukar tayar da hankali"
Kanwar gwamna mai suna Atsi Kefas ta samu harbin bindiga, inda da farko aka fara yi mata jinya a asibitin koyarwa na gwamnatin tarayya da ke Wukari kafin a dauke ta zuwa Abuja domin ci gaba da kula da lafiyarta.