Yadda za a iya kaurace wa mutuwa a yayin turmutsutsi na rarraba kayan tallafi - Ministan Jin kai



 Ministar ayyukan jin kai, da magance ibtila'i da jin dadin al’umma, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya bayyana wasu ka’idojin da ya kamata masu shirya taron rabon tallafi su rika bi, don gujewa turmutsutsi da zai haifar da mace-mace  

Ministan wanda ya bayyana haka a hirar da yayi gidan talabijin na Channels  Litinin, ya ce ya kamata a kiyaye ka'idoji irin su shigar da jami'an tsaro, hasashen matsalolin da za a iya fuskanta da tattara bayanan mahalarta taron da  sauransu.

Wadannan shawararwarin na Nentawe Yilwatda, na zuwa ne, biyo bayan mutuwar mutane da dama lokacin rabon tallafin kayan abinci a Abuja da Ibandan da Anambra a makon jiya.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp