Wayoyin lantarki |
Wani da ake zargin da laifin satar wayar lantarki Muktar Rabiu, wuta ta kama shi a lokacin da yake kokarin satar wayoyin lantarki a Abuja.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan birnin Abuja, Josephine Adeh, ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin.
A cewarta, lamarin ya faru ne makwanni kadan bayan an kama Rabiu, tare da yanke masa hukunci kan irin wannan laifin.