Wuta ta katse a Nijeriya bayan da kamfanonin sarrafa gas suka daina ba wa kamfanonin samar da lantarki

Wuta ta katse a Nijeriya bayan da kamfanonin sarrafa gas suka daina ba wa kamfanonin samar da lantarki

Wani bincike da jaridar PUNCH ta gudanar ya nuna cewa kamfanonin da ke samar da gas sun dakatar da bai wa kamfanonin samar da wutar lantarki iskar gas, sakamakon rashin biyan basussukan da aka tara musu tsawon lokaci. 

Babbar jami’ar kungiyar kamfanonin samar da wutar lantarki, Dakta Joy Ogaji, ce ta sanar da hakan a wata tattaunawa da jaridar PUNCH a ranar Laraba, inda ta jaddada cewa kamfanonin da ke samar da iskar gas sun sanar da daukacin kamfanoninsu a hukumance cewa sun dakatar da samar musu da iskar gas. 

An dai dakatar da samar da iskar gas din ne bayan da hukumar kula da harkokin man fetur ta Nijeriya ta umarci masu samar da iskar gas din da su daina ba wa kamfanonin samar da lantarki da ake bin su bashi.

Wannan lamarin dai shi ne ya haifar da katsewar wutar lantarki a fadin Nijeriya, wanda a halin yanzu, sama da kashi 70 cikin 100 na wutar lantarkin kasar ana samar wa ne ta hanyar iskar gas.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp