Hukumar Kididdiga a Nijeriya NBS ta fitar da wani rahoto na satar waya sama da miliyan 25 tsakanin watan Maris 2023 da zuwa Afrilu na shekarar 2024.
Rahoton ya nuna cewa kashi bakwai cikin 10 da aka sace ma waya a cikin gida ne ko wuraren taruwar jama'a.
Kashi 10 cikin 100 na mutanen da aka sace masu waya suka kai rahoto ga ‘yan sanda, yayin da kashi 90% suka kasa kai rahoto ga hukuma saboda wasu dalilai na kashin kansu.
Category
Labarai