Mai shari'a Maryanne Anenih ta kotun babban birnin tarayya Abuja ta bada tsohon gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello akan tsabar kudi N500 da kuma gabatar da mutum uku da za su tsaya masa.
Wannan na zuwa ne bayan da a makon da ya wuce wata kotun, karkashin jagorancin Mai shari'a Emeka Nwite ta bayarda belin Yahaya Bello a kan wadannan sharuddan.
Tsohon gwamnan na fuskantar tuhume-tuhume a kotunan biyu kan zargin badakalar kudade biliyan 110 da kuma wasu biliyan 80.