Wani abu mai hatsari har biyu ya sake fashewa a Zamfara

Akalla ababen fashewa biyu da 'yan bindiga suka dasa, sun tashi a wuri biyu dake cikin Dansadau a karamar hukumar Maru jihar Zamfara.

Fashewar ta afku ne a kan hanyar Dansadau zuwa Malamawa da kuma hanyar Malele duk a cikin yankin Dansadau bayan da wata motoci su ka taka abin fashewar sai dai babu asarar rayuka.

Zuwa lokacin rubuta wannan labarin, jaridar Premium Times bata samu ji daga mai magana da yawun rundunar 'yan sandan Zamfara ba saboda lambarsa bata zuwa.

Ko ranar Laraba wani abin fashewa ya yi sanadiyar mutuwar mutane 12 a karamar hukumar Maru, lamarin da rundunar 'yan sanda ta ce Lakurawa ne ke kokarin tsallakawa zuwa Dajin Birnin Gwari.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp