Vinicius Jr ya zama gwarzon dan wasan kwallon kafa na duniya

Dan wasa Vinicius Jr

Hukumar kwallon kafa ta Duniya FIFA ta kaarrama dan wasan  gefe na kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid da tawagar Brazil Vinicius Jr a matsayin gwarzon dan  wasa na shekara ta 2024.

Dan wasan mai shekaru 24 a baya dai yana cikin jerin yan wasan da suka yi takarar gwarzon dan wasan kwallon kafa na Duniya wato Ballon d'Or, wanda dan wasa Rodri na Manchester City ya lashe.

Vinicius dai ya taimaka wa kungiyarsa ta Madrid wajen lashe gasar zakarun Nahiyar Turai da ta La Liga na kakar shekerar 2023-24, inda ya ci kwallaye 24 tare da taimakawa a zura kwallo har sau 11.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp