Ƙunduma wa wani zagi a shafukan sada zumunta babban laifi ne - Rundunar 'Yan Sandan Nijeriya


Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan Nijeriya Olumuyiwa Adejobi, ya yi Allah wadai akan yadda wasu mutane ke ƙundumawa juna zagi a kan yanar gizo, yana mai cewa hakan babban laifi ne na cin zali karkashin dokar laifukan yanar gizo.

A cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, Adejobi ya ce mutanen da ke irin wadannan zage-zagen a kafofin sada zumunta ba su da kariya ta 'yancin fadin albarkacin baki ko suka.

Sai dai a martanin da wani ya mayar, mai shafin #kingkhone4real, ya ce in ko haka ne duk 'yan Nijeriya ya kamata a ce su na gidan kaso.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp