Zababben shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana shirinsa na korar miliyoyin bakin hauren da ba su da takardun izinin zama a kasar.
Baya ga haka, Trump ya ce zai sanya haraji kan kasashen ketare da ke huldar kasuwanci da kasar Amurka da kuma yin afuwa ga mutanen da aka yankewa hukunci saboda kutsawa a ginin majalisar kasar "Capitol" a ranar 6 ga Janairun shekarar 2021.
Trump ya sanar da wadannan tsare-tsaren ne lokacin da ya ke bayyana ajandojin gwamnatinsa, a yayin wata hira da gidan talabijin na NBC news.
Category
Ketare