Shugaban Nijeriya Bola Tinubu |
Shugaban Nijeriya Bola Tinubu zai gabatar da kudirin kasafin kudin shekarar 2025 na naira tiriliyan 47 da Biliyan 900 ga Majalisun dokokin kasar.
Shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio, ne ya bayyana hakan a zaman majalisar na ranar Alhamis.
A 'yan makwannin da suka gabata ne Tinubu ya gabatarwa majalisun biyu, daftarin kasafin kudin na matsakaicin zango da ya kai Naira tiriliyan 26 da biliyan 100.